Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    BECHI HAUSA NEWSBECHI HAUSA NEWS
    • Shafin Farko
    • Labarai

      Tanka Ta Murƙushe Mutane 5 a Gombe

      January 12, 2026

      Babu Siyasa a Binciken Da Ake Yi Wa Malami – EFCC

      January 12, 2026

      Ƴan Bindiga Sun Kashe Soja Da Jam’in NSCDC a Benue

      January 12, 2026

      Manyan Jiga-jigan APC 3 a Kogi Sun Mutu

      January 12, 2026

      INEC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Ɓatan Naira Biliyan 55.9 a Zaben 2019

      January 12, 2026
    • Siyasa

      Manyan Jiga-jigan APC 3 a Kogi Sun Mutu

      January 12, 2026

      Ganduje Zai Gana Da Masu Ruwa-da-tsaki Na APC

      January 11, 2026

      Datti Baba-Ahmed Ya Musanta Batun Tsayawa Takarar Shugaban Ƙasa

      January 9, 2026

      Fubara Barazana Ne Ga Demokaraɗiyya – Kakakin Majalisar Rivers

      January 9, 2026

      Kotu Ta Ƙi Bayar da Belin Kwamishinan Kuɗi Na Bauchi

      January 6, 2026
    • Addini

      Kano: Hisbah Ta Karɓi Ƙorafe-Ƙorafe Sama da 12,000 a 2025

      January 2, 2026

      Da Ɗumi-ɗumi : Sheikh Dahiru Bauchi Ya rasu

      November 27, 2025

      Zakaran Gwajin Dafi : Hajji 2025 Karkashin Farfesa Saleh Pakistan  

      November 24, 2025

      Hajji Da Shugabanci Nagari Ƙarƙashin Jagorancin Farfesa Pakistan

      November 17, 2025

      Hukumar NAHCON Ta Sanar Da Rage Kudin Aikin Hajjin 2026

      November 10, 2025
    • Nishadi

      Oculus Founder Makes a VR Headset That Can Literally Kill You

      January 13, 2021
      85

      Braun Series 7 Electric Shaver Review: Quality at a Good Price

      January 13, 2021
      85

      Google Pixel 7, iPhone 14 Compared: Check Out 5 Major Differences

      January 13, 2021

      Why Apple Should Skip The MacBook Pro Launch

      January 12, 2021

      Apollo G2J Showcases Electric Sports Car

      January 12, 2021
    • Tsaro

      Sojojin Najeriya Sun Ƙwato lita 290,000 Na Man Fetur a Yankin Neja Delta

      October 21, 2025

      Ƴan Bindiga Sun Ƙwace Wayoyin Ƴan Sanda a Zamfara

      October 2, 2025

      Gwamnan Kano Ya Buƙaci Tinubu Ya Tsige Kwamishinan Ƴan Sandan Jihar

      October 1, 2025

      Will Using a VPN on Phone Helps Protect You from Ransomware?

      January 14, 2021

      Popular New Xbox Game Pass Game Being Review Bombed With “0s”

      January 14, 2021
    BECHI HAUSA NEWSBECHI HAUSA NEWS
    Home » Hajji Da Shugabanci Nagari Ƙarƙashin Jagorancin Farfesa Pakistan
    Addini

    Hajji Da Shugabanci Nagari Ƙarƙashin Jagorancin Farfesa Pakistan

    Abbass AbdurrahmanBy Abbass AbdurrahmanNovember 17, 2025No Comments5 Mins Read

    Rubutu na Musamman

    Daga

    Muhsin Tasi’u Yau

    A yau, duniya ta zama wuri guda. Fasaha ta sauya yadda muke tafiya, yadda muke koyon abubuwa, da yadda muke gudanar da manyan ayyuka. Hajj, duk da kasancewarsa ibada ce mai dindindin tun zamanin Annabawa, ya zama wani babban tsari na zamani da ake gudanarwa cikin hanyoyi masu fasaha da tsarin gudanarwa na ƙwararru. A ƙasarmu Nijeriya, wannan sabon salo ya fara bayyana sosai a shekarun baya-bayan nan. Amma a ga sauyi tare da tasirinsa a qanqanin lokaci sai lokacin jagorancin shugaba na gari abin koyi Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan wanda ya tsaya tsayin daka don samar da shugabanci da ayyukan hajji mai tafe da zamani.

    SABUWAR DUNIYAR HAJJ: TA FASAHA DA TSARI

    Alhazai a yanzu ba sa buƙatar dogon takardu da fam-fam kamar da. Rajista da bayanai sun koma ta kan layi (online). Takardu, bayanan lafiya, jadawalin tashi, har ma da horon manasik, ana samun su a wayar hannu. Wannan sabon sauyi ya rage cunkoso, ya rage ruɗani, ya kuma taimaka wajen sauƙaƙa wa jama’a.

    A tsahon shekara guda na zaman Farfesa Pakistan a shugancin hukumar, Hajj ya koma abu mai tsari sosai wanda ya haɗa gwamnati, kamfanonin jiragen sama, cibiyoyin kiwon lafiya, jami’an tsaro, da hukumomin Saudiyya. Wannan haɗin gwiwa na zamani ne ke tabbatar da cewa duk wanda ya shirya, zai iya tafiya cikin sauƙi.

    DAGA GIDA ZUWA FILIN JIRGI: HORO DA TAIMAKO SUN SAUYA

    Matakin farko na Hajj a yau yana farawa da horo ta zamani. Tsofaffi da matasa da maza da mata duk suna samun bayanai ta WhatsApp, YouTube, rubutun bidiyo, da taron kai tsaye. Wannan ya rage tsoron da ake yi wa Hajj, musamman ga masu tafiya a karon farko. A filin jirgin sama kuma, alhazai na samun taimako kai tsaye. Ana taimaka musu da kaya, ana nuna musu hanyoyi, ana gyara musu takardu, ana tabbatar da jin dadin su kafin tashi. A nan ma an samu sauyi sosai a qa ake ganin yadda aikin Hajj ya sauya daga tsarin gargajiya zuwa tsarin zamani, mai cike da kulawa da bin ka’ida.

    ZUWA SAUDIYYA: KULAWA A MATAKI-MATAKI

    Da zarar alhazai sun isa Saudiyya, tsarin zamani ya ci gaba da aiki. Motoci, masauki, jadawalin manasik komai yana bi ta tsarin da aka tsara tun daga gida. Jami’ai su na nan a kowane lokaci domin warware matsaloli cikin gaggawa. A ƙasashen da jama’a ke da yawa irin tamu, tsarin ya zama mafi muhimmanci. Domin inda ake tafiyar da dubban mutane lokaci guda, sai an yi aiki cikin tsari kamar yadda ake yi wajen manyan taron duniya. Duk da haka, Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan ya yi matuqar qoqari don ganin alhazan Nijeriya ba su fuskanci kowacce irin matsala ba.

    FASAHA TA SAUYA RAYUWAR ALHAZAI

    Zamani abokin tafiya . Wannan ma’aikatar a qarqashin jagorancin Prof Pakistan Akwai abubuwan zamani da alhazai suka ci gajiyarsa a lokacinsa. Misali:

    Aikace-aikacen wayar hannu don neman hanya,

    Taswirar masauki da motoci,

    Labaran lokaci-lokaci ta sakon waya,

    Tsarin gaggawa domin magance matsalolin lafiya,

    Jerin laccoci da bidiyo na koyon manasik.

    Wannan sabuwar fasaha ta sa Hajj ya zama mai sauƙi fiye da baya, musamman ga matasa masu son fahimtar komai cikin hanzari.

    JAGORANCI A ZAMANIN YANZU: BA MULKI SAI HIDIMA

    Halin mutum jarinsa. Sannan amfanin ilimi aiki da shi. Ba sai an tsawaita bayani ba, duk wanda ya san shugaban hukumar alhazai ta qasa Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan ya san malami ne mai tawadhi’u da son jama’a da yi musu hidima a kan kansa bare kuma in an wakilta shi. Wannan ta sa tunda aka ba shi wannan jagorancin bai zauna ba har sai da ya tabbatar an yi aikin hajji lafiya da nutsuwa an kammala lafiya. Haka cikin girmamawa da mutunta juna. A zamanin da muke ciki, jama’a musamman matasa na kallon jagoranci ta wani sabon fuska. Jagora na zamani shi ne wanda yake sauka kasa, yana tattaunawa, yana lallashi, yana sauraro, yana gyarawa. Ayyukan Hajj sun zama wata hanya da ake ganin irin wannan jagoranci wanda ke ba da kulawa ga kowa, ba tare da nuna bambanci ba. Bayan haka, aikin Hajj yana buƙatar jagoranci mai natsuwa, wanda ke iya yin aiki da manyan hukumomi, kasashe, da dubban mutane a lokaci guda. Wannan yana nuna irin ƙwarewar da ake buƙata wajen gudanar da harkokin al’umma a zamanin yau. Shakka babu in ana buqatar hoton wannan jagora to shi ne Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan

    KAMMALAWA

    “Hasken Hajj a Zamaninmu” na nuni da yadda aikin Hajj ya sauya, ya tsaru, ya zamanantu, kuma ya ci gaba da bayar da darasi ga kowa. Ya nuna cewa addini ba tare da tsari ba yana iya zama wahala, kuma zamani ba tare da mutunci da ibada ba zai rasa tushe. Don haka wajibi ne a jinjinawa wannan shugaban hukumar Alhazai ta qasa (NAHCON) Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan.

    Hajj ya zama haɗin kai ne tsakanin tsohon tarihi da sabuwar fasaha. Ya zama alamar yadda muke tafiya daga gida zuwa ƙasa mai tsarki cikin kulawa, tsaro, natsuwa, da fahimta. Wannan hasken ne ya ke canza yadda ake gudanar da Hajj a wannan lokacin shugabancin Farfesa Pakistan kuma shi ne hasken da zai ci gaba da haskaka gaba.

    Hajji
    Share. Facebook Twitter WhatsApp Telegram
    Previous ArticleTuraki Ya Zama Sabon Shugaban Jam’iyyar PDP Na Ƙasa
    Next Article Gwamnan Akwa Ibom Ya Ware Naira Miliyan 800 Domin Inganta Rayuwar Hausawa Da Yarabawa a Jihar
    Abbass Abdurrahman
    • Website

    Related Posts

    Featured

    Tanka Ta Murƙushe Mutane 5 a Gombe

    January 12, 2026
    Featured

    Babu Siyasa a Binciken Da Ake Yi Wa Malami – EFCC

    January 12, 2026
    Featured

    Ƴan Bindiga Sun Kashe Soja Da Jam’in NSCDC a Benue

    January 12, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    SABBIN LABARAI

    Gwamnatin Kano Ta Dakatar da Malam Lawan Triumph Daga Yin Wa’azi

    October 1, 202542 Views

    Kotu Ta Yankewa Tsohon Firayim Ministan Mali Hukuncin Zaman Gidan Yari Sakamakon Rubutu a Shafin Sada Zumunta

    October 27, 202541 Views

    Dantawaye Ya Zama Sabon Kwamishinan Ƴansanda a Abuja

    October 17, 202532 Views

    An Gano Motar Ofishin Mataimakin Gwamna Da Aka Sace

    November 12, 202527 Views

    NAFDAC Ta Yi Gargaɗi Kan Wani Kororon Roba Me Matuƙar Haɗari Ga Lafiya

    December 30, 202525 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    • Telegram
    © 2026 Bechi Hausa News. Developed by: ENGRMKS & CO.
    • Shafin Farko
    • Game da Mu
    • Ƙarin Bayani
    • Manufar Sirri
    • Ka’idoji da Sharudda
    • Tuntuɓe Mu

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.