Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    BECHI HAUSA NEWSBECHI HAUSA NEWS
    • Shafin Farko
    • Labarai

      Ba Kama Gbajabiamila Muka Yi Ba Gayyatarsa Muka Yi – ICPC

      July 21, 2026

      Tinubu Ya Naɗa Sabbin Shugabanni Da Mambobi 26 a Hukumomi Da Kwamitocin Gwamnatin Tarayya

      July 21, 2026

      An Zargi Likitan El-Rufai Da Bayar da Rahoton Jinya Na Bogi

      July 21, 2026

      Guguwa Da Ruwan Sama Mai Ƙarfi Sun Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane Huɗu a Sakkwato

      July 21, 2026

      Mamakon Ruwan Sama Ya Lalata Gidaje Da Gonaki a Filato

      July 20, 2026
    • Siyasa

      Kotu Ta Yi Watsi da Ƙarar da Tsagin Tanimu Turaki Suka Shigar Kan Rikicin Shugabancin PDP

      July 18, 2026

      Ya Kamata Majalisa Ta Yi Bincike Kan Ingancin Lafiyar Tinubu – ADC

      July 17, 2026

      Gwamna Yusuf Ya Zaɓi Garo a Matsayin Mataimakinsa a Zaɓen 2027

      July 13, 2026

      INEC Ta Ƙara Wa’adin Miƙa Sunayen ‘Yan Takarar Zaɓen 2027

      July 12, 2026

      Sauye-sauyen Gwamnatina Sun Inganta Ayyuka Da Tattalin Arziki a Kaduna – Gwamna Uba Sani 

      July 10, 2026
    • Addini

      An Rufe Birnin Tehran Domin Jana’izar Ayatollah Ali Khamenei

      July 1, 2026

      Kotu Ta Buƙaci a Gabatar Da Litattafan Da Sheikh Abduljabbar Ya Yi Amfani Da Su

      June 29, 2026

      NAHCON Ta Kammala Dawo Da Alhazan Najeriya Daga Saudiyya

      June 23, 2026

      Sarkin Musulmi Ya Buƙaci Hukumomi Su Gaggauta Ɗaukar Matakai Domin Magance Matsalar Tsaro

      June 17, 2026

      Gwamnatin Kano Za Ta Kashe Naira Biliyan 1.5 Domin Shirin ‘Auren Gata’

      June 15, 2026
    • Nishadi

      Oculus Founder Makes a VR Headset That Can Literally Kill You

      January 13, 2021
      85

      Braun Series 7 Electric Shaver Review: Quality at a Good Price

      January 13, 2021
      85

      Google Pixel 7, iPhone 14 Compared: Check Out 5 Major Differences

      January 13, 2021

      Why Apple Should Skip The MacBook Pro Launch

      January 12, 2021

      Apollo G2J Showcases Electric Sports Car

      January 12, 2021
    • Tsaro

      Sojoji Sun Kama Ƴan Ƙasashen Waje Da Ake Zargin Suna da Hannu a Matsalar Tsaron Najeriya – Bwala

      July 18, 2026

      ‘Yan Sanda Sun Fara Kwato Makaman Da Ke Hannun Jama’a Ba Bisa Ka’ida Ba – IGP Disu 

      July 17, 2026

      Sojoji Sun Gano Ƴan Ƙasashen Waje Uku Cikin Mayaƙan ISWAP a Borno

      July 13, 2026

      An Kashe Fitaccen Jagoran ‘Yan Bindiga Sani Yellow a Zamfara

      July 12, 2026

      Matasa a Borno Sun Gudanar Da Zanga-Zanga Kan Rashin Tsaro

      July 12, 2026
    BECHI HAUSA NEWSBECHI HAUSA NEWS
    Home » Ba Da Amincewar NNPP Gwamna Abba Zai Fita Daga Jam’iyya Ba – Dungurawa
    Featured

    Ba Da Amincewar NNPP Gwamna Abba Zai Fita Daga Jam’iyya Ba – Dungurawa

    Abbass AbdurrahmanBy Abbass AbdurrahmanDecember 29, 2025No Comments2 Mins Read

    Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano, Hon. Suleiman Hashim Dungurawa, ya bayyana cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da duk wasu da ake zargin za su bi shi zuwa jam’iyyar APC sun ɗauki wannan mataki ne bisa ra’ayinsu na kashin kansu. Ya ce shugabancin NNPP na jiha da ƙasa, tare da Jagoran jam’iyyar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ba su amince da irin wannan sauya sheƙa ba. Dungurawa ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Kano, ranar Litinin, da safe.

     

    Ya ƙara da cewa jam’iyyar ta yi iya ƙoƙarinta wajen ganin gwamnan da magoya bayansa sun janye wannan yunƙuri, domin mutunta jam’iyyar da kuma jama’ar Kano da suka ba su amana. A cewarsa, duk da roƙe-roƙe da nasihohi da aka yi, abubuwa sun ƙi juyawa, abin da ya sa ake ta yaɗa jita-jitar sauya sheƙar.

     

    Dungurawa ya sake roƙon gwamnan da masu shirin bin sa da su sake tunani, su “mayar da wuƙarsu kube,” su tsaya kan NNPP maimakon komawa jam’iyyar APC wadda ya ce jama’a da masu zaɓe sun yi watsi da ita. Ya yi wannan kira ne a madadin shugabanni da magoya bayan jam’iyyar baki ɗaya.

     

    Daga ƙarshe, shugaban NNPP na Kano ya karyata jita-jitar da ke alaƙanta shi da wasu jiga-jigan jam’iyyar da zargin haɗa Gwamna Abba Kabir Yusuf da Jagora Sanata Kwankwaso. Ya ce shi, mataimakin gwamna, Sanusi Surajo, Sanata Rufai Hanga da sauran su ba su taɓa haɗa kowa da jagora ba, yana mai kalubalantar duk mai iƙirarin haka da ya fito da hujja.

    NNPP
    Share. Facebook Twitter WhatsApp Telegram
    Previous ArticleGwamnatin Tarayya Ta Horas da Dakaru 7,000 Domin Daƙile Ta’addanci a Dazuka
    Next Article Ƴan Najeriya Za Su Ci Moriyar Rikicin Da Ake Kan Farashin Man Fetur — NNPCL
    Abbass Abdurrahman
    • Website

    Related Posts

    Featured

    Ba Kama Gbajabiamila Muka Yi Ba Gayyatarsa Muka Yi – ICPC

    July 21, 2026
    Featured

    Tinubu Ya Naɗa Sabbin Shugabanni Da Mambobi 26 a Hukumomi Da Kwamitocin Gwamnatin Tarayya

    July 21, 2026
    Featured

    An Zargi Likitan El-Rufai Da Bayar da Rahoton Jinya Na Bogi

    July 21, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    SABBIN LABARAI

    Ba Don Gudunmawar Masu Yiwa Ƙasa Hidima Ba Da Jihohi Dayawa Basu Kai Yadda Suke a Yanzu Ba – Minista

    December 8, 2025150 Views

    Sabon Rikici Ya Kunno Kai a NDC : Ƴan Takara Sun Kai Ƙara Kan Zaɓen Fidda-gwani a Kano

    June 30, 202679 Views

    Gwamnatin Kano Ta Dakatar da Malam Lawan Triumph Daga Yin Wa’azi

    October 1, 202546 Views

    Kotu Ta Yankewa Tsohon Firayim Ministan Mali Hukuncin Zaman Gidan Yari Sakamakon Rubutu a Shafin Sada Zumunta

    October 27, 202541 Views

    Dantawaye Ya Zama Sabon Kwamishinan Ƴansanda a Abuja

    October 17, 202533 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    • Telegram
    © 2026 Bechi Hausa News. Developed by: ENGRMKS & CO.
    • Shafin Farko
    • Game da Mu
    • Ƙarin Bayani
    • Manufar Sirri
    • Ka’idoji da Sharudda
    • Tuntuɓe Mu

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.