Hukumar NAFDAC ta ƙwace sama da magungunan zazzaɓin cizon sauro na bogi miliyan 10 tare da kayan kwalliya a wani farmaki da ta kai kasuwar baje koli a Jihar Lagos.
An kiyasta darajar kayan da aka ƙwace da kusan naira biliyan uku.
Daraktan bincike da aiwatar da doka na NAFDAC, Dr Martins Iluyomade, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Apapa ranar Litinin.
Ya ce an kai farmakin ne ƙarƙashin jagorancin shugabar hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye, bayan samun sahihan bayanan sirri a ranar 3 ga Fabrairu.
A cewarsa, kayan da aka ƙwace sun haɗa da magungunan zazzaɓin cizon sauro, alluran cerebral malaria, magungunan rigakafi, Postinor da Anagin, duk na bogi.
Ya ce an ɓoye su a wani gini mai hawa uku da aka bayyana a matsayin sito, inda aka kwashe lodin manyan motoci takwas tare da kama mutane huɗu, yayin da bincike ke ci gaba.

