Hukumar National Bureau of Statistics (NBS) ta sanar da cewa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya ragu zuwa kashi 15.10 cikin 100 a watan Janairun 2026, alamar da ke nuna sauƙi idan aka kwatanta da yadda tsadar rayuwa ta yi kamari a baya.
Hukumar ta bayyana cewa wannan raguwa ya biyo bayan sauya tsarin lissafin farashin kayayyaki domin ya dace da sabon yanayin kasuwanci, inda aka mayar da ma’aunin zuwa tsarin kasuwancin shekarar 2024. Wannan sauyi ya sa sabon ƙididdigar ta yi ƙasa idan aka kwatanta da kashi 27.61 cikin 100 da aka samu a bara.
Shugaban hukumar, Prince Adeyemi Adeniran, ya ce sabon tsarin ne ya haifar da raguwar alƙaluman. Sai dai masana sun yi gargadi cewa raguwar ƙididdigar ba yana nufin farashin kayayyaki a kasuwanni ya sauka gaba ɗaya ba, domin har yanzu jama’a na iya ci gaba da fuskantar tsadar rayuwa.

