Wani matashi mai suna Ahmad Dankoli ya rasa ransa bayan da wasu fusatattun matasa suka zarge shi da yunƙurin satar babur a garin Balare da ke Ƙaramar Hukumar Ajingi a Jihar Kano. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na daren Lahadi, yayin da kasuwar garin ke ci.
Rahotanni sun ce bayan mutuwarsa, wasu daga cikin matasan sun ƙwace gawarsa daga hannun jami’an tsaro tare da banka mata wuta. Kansilan Mazabar Balare ya ce yawaitar satar babura a yankin, inda sama da babura 32 suka ɓace cikin ’yan watanni, na daga cikin abubuwan da suka tayar da hankalin al’umma.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce har zuwa lokacin da aka tuntube shi ba a kai rahoton lamarin ofishin ’yan sanda ba, amma ya tabbatar rundunar za ta gudanar da bincike.

