undunar ’Yan Sandan Jihar Sakkwato ta ce ta daƙile wani hari da ake zargin ’yan bindiga sun kai ƙauyen Daraye da ke Ƙaramar Hukumar Wamakko, inda jami’an suka kashe mutum ɗaya da ake zargin ɗan bindiga ne tare da ƙwato bindigar AK-47 da harsasai.
Rundunar ta bayyana cewa ta samu kiran gaggawa kan harin, lamarin da ya sa jami’an sashen yaƙi da masu garkuwa da mutane da sauran ƙungiyoyin musamman suka garzaya yankin. Bayan musayar wuta, maharan sun tsere zuwa cikin daji da raunukan harbin bindiga.
’Yan sandan sun ce an ƙara tsaurara sintirin tsaro a yankin tare da sanya ofisoshin da ke maƙwabtaka cikin shirin ko-ta-kwana domin cafke waɗanda suka tsere. Kakaki24 na ci gaba da bibiyar wannan lamari.

