Majalisar Dattawa ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta dakatar da shirin gyara da sake mayar da tubabbun ’yan Boko Haram da sauran masu aikata laifuka cikin al’umma. Bukatar ta biyo bayan kudirin da aka gabatar kan karuwar hare-hare, sace-sace da kashe jami’an soja masu ritaya da masu aiki.
Sanatocin sun nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro a sassan kasar nan, tare da yin Allah wadai da ci gaba da gyarawa da sake shigar da ’yan ta’adda, ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane cikin al’umma. Sun kuma bukaci hukumomin tsaro su kara inganta tattara bayanan sirri da amfani da fasahar zamani wajen yaki da ta’addanci.
Sai dai wani kwararren masanin tsaro, Dakta Babayo Sule, ya soki matsayar Majalisar Dattawa, yana mai cewa dakatar da shirin ba zai magance matsalar tsaro ba. Ya ce maimakon soke shirin, ya kamata a gyara kura-kuransa tare da karfafa aiwatar da shi domin samun zaman lafiya mai dorewa.

