Mutumin da ke ikirarin shi ne Darakta Janar na Hukumar Presidential Foreign Investment Promotion Council (PFIPC), Prince Adeniyi Adeyemi, ya bayyana cewa a shirye yake ya ba Hukumar ICPC cikakken hadin kai wajen binciken da aka kaddamar kan hukumar da Fadar Shugaban Kasa ta ce babu ita.
Adeyemi ya ce zai mika duk wasu takardun da ke hannunsa ga jami’an tsaro domin taimaka wa binciken, yana mai cewa hakan zai bayyana yadda aka kafa hukumar da kuma ko an bi ka’idojin gwamnati. Ya kuma ce yana mamakin yadda aka sanya hukumar cikin kasafin kudin kasa duk da ikirarin cewa ba a kafa ta ba.
Haka kuma, Adeyemi ya ce ya fi son a bar kwamitin bincike mai zaman kansa ya gano gaskiya kan zarge-zargen da ya yi, maimakon ci gaba da yin karin bayani. A gefe guda, Shugaba Bola Tinubu ya umarci ICPC ta binciki dukkan ayyukan da ake zargin hukumar ta gudanar tare da mika rahoto cikin kwanaki 30.

