Rundunar sojin Najeriya ta ce ta gano wasu ƴan ƙasashen waje uku cikin mayaƙan ISWAP da ke taimaka wa ƙungiyar wajen tsara hare-hare a Najeriya. Rundunar Operation Haɗin Kai ta bayyana cewa an gano mutanen ne bayan ƙwace wata kyamara a wani gumurzu da aka yi da mayaƙan ƙungiyar a yankin Cross Kauwa na Jihar Borno.
A cewar rundunar, cikin mutanen da aka gano akwai wani Bafalasɗine mai suna Abu Ishaq, wanda ta bayyana a matsayin babban mai horas da mayaƙan ISWAP. Haka kuma an gano wani mai suna Abu Thaiba, wanda aka ce shi ne likitan ƙungiyar, yayin da ake ci gaba da binciken bayanan wani mutum na uku.
Rundunar ta ce kyamarar da aka ƙwato ta ƙunshi hotuna da bayanan yadda mayaƙan ISWAP ke tsara hare-hare kan sansanonin soji. Ta ƙara da cewa ɗaya daga cikin masu ɗaukar hotunan ƙungiyar ne ya jefar da kyamarar yayin fafatawar da aka yi da sojoji.

