Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana cewa kusan kashi 40 cikin 100 na ɗaliban da ke halartar makarantun gwamnati na zuwa ne saboda shirin ciyar da ɗalibai kyauta. Ta ce shirin na taka muhimmiyar rawa wajen rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, musamman almajirai.
Babbar Mataimakiya ta Musamman ga Gwamna Uba Sani kan shirin ciyar da ɗalibai, Fauziya Buhari-Ado, ta bayyana hakan bayan karɓar lambar yabo kan bunƙasa ilimi. Ta ce gwamnatin ta ɗauki matakan gyara tun daga farkon mulkinta domin ƙarfafa ilimin kyauta da shirin ciyar da ɗalibai.
Buhari-Ado ta ce ziyarce-ziyarcen da ake kai wa makarantu sun nuna cewa shirin ya ƙara yawan masu shiga da ci gaba da zama a makaranta. Ta kuma yaba da yadda gwamnatin jihar ke zuba jari a fannin ilimi, gine-ginen makarantu da shirye-shiryen tallafa wa yara domin inganta karatu da walwalar ɗalibai.

