Iyayen ɗaliban da aka sace a jihar Borno sun roƙi Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Babagana Zulum su ƙara ƙaimi wajen ganin an kuɓutar da ‘ya’yansu da sauran waɗanda aka yi garkuwa da su, bayan shafe kwanaki 100 a hannun masu garkuwa da su.
An sace ɗalibai 42 na Mussa Primary da Junior Day Secondary School a Askira-Uba ranar 15 ga Mayu 2026, yayin da aka sace wasu ɗalibai 36 na Government Day Secondary School da ke Lassa ranar 29 ga Yuni. Iyayen sun kuma nemi ceto mutane 38 da aka sace a hanyar Buratai zuwa Maiduguri.
A wani taron manema labarai ranar Juma’a, Sakataren Hawul/Askira-Uba Elders Forum, Malla Gadzama, ya bayyana halin da iyalan ke ciki a matsayin na tsawaitaccen ciwo, tsoro da rashin tabbas. Sun kuma buƙaci a samar da hanyoyin sadarwa na gaskiya domin iyalai su riƙa samun bayanai kan ƙoƙarin ceto waɗanda aka sace.
Iyayen sun ce bai kamata a bar sace yaran ya zama wani abu na yau da kullum ba, inda suka roƙi gwamnati ta yi amfani da dukkanin hanyoyin tsaro da ake da su wajen ceto waɗanda aka yi garkuwa da su. Sun kuma buƙaci a ƙara tsaron makarantu, manyan hanyoyi da yankunan da ke cikin haɗari.

