Rundunar ’yan sandan jihar Kaduna ta gurfanar da mutum 24 a gaban kotun majistare bisa zarginsu da hannu a kisan wata matar aure da wasu fusatattun mutane suka yi a yankin Maraban Jos.
Ana tuhumar waɗanda ake zargin da laifukan bayar da gudummuwa wajen aikata laifi, tayar da hankalin jama’a, lalata dukiyoyi, lalata kadarorin gwamnati da na ’yan sanda, da kuma kisan kai. ’Yan sanda sun ce an gurfanar da su ne bayan binciken da suka gudanar kan lamarin da ya faru a ranar 21 ga Yunin 2026.
Kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 21 ga Yulin 2026, tare da umarnin a tsare dukkan waɗanda ake zargin a gidan yari har zuwa lokacin ci gaba da shari’ar. Rundunar ta ce har yanzu ana binciken sama da mutum 100 da ake zargin suna da hannu a lamarin, tare da alƙawarin gurfanar da duk wanda aka samu da laifi.

