Akalla mutane 21 ake fargabar sun mutu, yayin da wasu 37 aka yi garkuwa da su bayan ‘yan bindiga dauke da makamai sun kai hari garin Tsamaye da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto. Harin ya kuma tilasta wa dubban mazauna yankin barin gidajensu.
Shaidu sun ce harin ya fara ne da misalin ƙarfe 9:00 na daren Litinin, ya ci gaba har zuwa bayan ƙarfe 3:00 na safiyar Talata. An ƙona gidaje biyu, an sace dabbobi, yayin da al’ummar garin suka tsere.
A yayin yunƙurin tserewa daga harin, wasu mazauna garin sun shiga cikin wani kogi, inda kwale-kwalen da suka cika da mutane suka kife. Kimanin mutane 25, mafi yawansu mata da yara ne suka nutse; an ceto bakwai, yayin da ake fargabar 18 sun nutse.
Shugaban ƙaramar hukumar Sabon Birni, Ayuba Hashimu, ya tabbatar da faruwar harin, amma ya ce ba zai iya tabbatar da adadin waɗanda suka mutu ko aka sace ba. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufai, ya ce an tura ƙarin jami’an tsaro domin dawo da zaman lafiya da hana sake kai hare-hare.

