Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ayyana Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar Asabar.
Adeleke, wanda ya yi takara a ƙarƙashin jam’iyyar Accord, ya samu kuri’u 511,067, inda ya yi nasara a ƙananan hukumomi 19 daga cikin 30 na jihar. An ayyana sakamakon ne da misalin ƙarfe 7:24 na safiyar Lahadi.
Babban abokin hamayyarsa, Bola Oyebamiji na jam’iyyar APC, ya samu nasara a ƙananan hukumomi 11. Adeleke ya yi nasara a Ede North, Ede South, Ejigbo, Iwo, Egbedore, Ife North da Ife East, da wasu ƙananan hukumomi.
Jami’in tattara sakamakon zaɓen, Farfesa Joshua Ogunwole, ya bayyana Adeleke a matsayin wanda ya cika ƙa’idojin doka, tare da mayar da shi kan kujerar gwamna na wani wa’adin mulki.

