Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ƙara ƙaimi wajen magance matsalar tsaro a ƙasar, yana mai jaddada cewa ba za a bari rashin tsaro ya dusashe nasarorin da aka samu ba. Ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi Mataimakin Shugaban ƙasa da gwamnoni 23 a gidansa da ke Legas domin bikin Eid-el-Fitr.
Tinubu ya ce ya tattauna da shugaban Faransa, Emmanuel Macron, kan samar da kayan aiki da tallafin tsaro, tare da ƙoƙarin haɗa kai da sauran ƙasashe. Ya kuma nuna damuwa kan yadda rikicin Gabas ta Tsakiya zai iya jawo hauhawar farashi da rage ƙarfin sayen jama’a, yana mai kira ga gwamnatocin jihohi su ɗauki matakai don rage tasirin hakan.
Shugaban ya buƙaci gwamnoni su ci gaba da haɗin kai da juriya wajen aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da za su amfani jama’a, tare da tallafa wa gwamnati wajen yaƙar matsalar tsaro. A nasa ɓangaren, shugaban ƙungiyar gwamnoni, AbdulRahman AbdulRazaq, ya yabawa shugaban ƙasa kan ziyararsa zuwa Birtaniya da kuma yarjejeniyoyin zuba jari da aka cimma.

