Wasu dattawa a Jihar Katsina sun buƙaci a gaggauta sakin masanin harkokin tsaro kuma mai sharhi kan al’amuran jama’a, Dr. Bashir Usman Kurfi, ba tare da wani sharadi ba. Sun ce kama da tsare shi na iya kawo cikas ga ƙoƙarin da ake yi na magance matsalar tsaro a jihar.
A cikin wata sanarwa da Dr. Hassan Garba ya sanya wa hannu a madadin ƙungiyar, dattawan sun ce Dr. Kurfi ya dade yana ba da gudunmawa wajen yaƙi da ƴan bindiga da sauran masu aikata laifuka ta hanyar haɗin gwiwa da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.
Dattawan sun yi kira ga gwamnatin Jihar Katsina da ta mayar da hankali wajen kamo da gurfanar da ƴan bindiga maimakon tsare mutanen da ke bayar da shawarwari da bayanan da ke taimakawa wajen samar da zaman lafiya. Sun ce sakin Dr. Kurfi zai ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki wajen yaƙi da rashin tsaro.

