Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya rabawa ƙungiyoyin ‘Yan Akwati daga ƙananan hukumomi 44 na jihar filaye sama da 1,500, a wani shiri da aka bayyana a matsayin irinsa na farko.
Rabon filayen ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Filaye da Tsare-tsaren Gine-gine na Jihar Kano, Hon. Abduljabbar Muhammad Umar Garko. Gwamnatin jihar ta ce shirin na daga cikin matakan tabbatar da gaskiya, adalci da ƙwarewa wajen gudanar da harkokin filaye.
Gwamna Abba ya bayyana cewa shirin na daga cikin muhimman alƙawuran da gwamnatinsa ta ɗauka yayin yaƙin neman zaɓe, tare da nufin bai wa jama’a damar mallakar filaye ta hanyoyin da doka ta tanada da kuma ƙarfafa tsarin gine-ginen birane.
Kwamishinan Filaye da Tsare-tsaren Gine-gine, Abduljabbar Muhammad Umar, ya ce shirin zai taimaka wajen faɗaɗa damar mallakar filaye, rage ƙarancin gidaje da dakile kwace filaye da sayar da su ba bisa ka’ida ba. Ya kuma shawarci waɗanda suka amfana da su ɗauki filayen a matsayin jarin iyali na dogon lokaci.

