Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana shirin gwamnatinsa na kafa kamfanin jiragen sama mallakin jihar domin samar da ayyukan yi ga matukan jirgi ‘yan asalin Kano da suka kammala horon ƙwarewa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin taron Majalisar Zartarwa karo na 40 da aka gudanar a Fadar Gwamnatin Kano, inda ya karɓi lambobin yabo da dama, ciki har da wanda Ƙungiyar Matukan Jiragen Sama ta Jihar Kano ta ba shi saboda goyon bayan da yake bai wa mambobinta.
Ya ce da yardar Allah, ana sa ran kamfanin jiragen saman na Kano zai fara aiki cikin shekara guda mai zuwa, yana mai tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta samar da dukkan goyon bayan da ake buƙata domin ganin an aiwatar da shirin cikin nasara.
A nasa jawabin, Shugaban Ƙungiyar Matukan Jiragen Sama ta Jihar Kano, Naziru Ibrahim, ya yaba wa gwamnan kan tallafin da yake bai wa matukan jirgin, tare da roƙon gwamnatin da ta taimaka musu wajen samun takardun shaidar ƙarshe da za su ba su damar gudanar da zirga-zirgar jiragen kasuwanci a Najeriya da ƙasashen waje.

