Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sauke Shugaban Ma’aikatan Jihar, Abdullahi Musa, daga mukaminsa nan take. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a yammacin ranar Talata.
Sanarwar ta ce matakin na daga cikin kokarin gwamnatin jihar na sake fasalin aikin gwamnati domin inganta aiki, karfafa ladabtarwa da kuma samar da ingantaccen aiki a hukumomin gwamnati. Gwamnan ya kuma gode wa tsohon Shugaban Ma’aikatan bisa gudunmawa da jajircewarsa wajen yi wa jihar hidima a lokacin da yake kan mukami.
Hakazalika gwamnan ya umarci Hajiya Bilkisu Shehu Maimota, Babbar Sakatare a Sashen Gudanarwa da Ayyuka na Ofishin Majalisar Zartarwa, da ta rike mukamin Shugabar Ma’aikatan Jihar na rikon kwarya har sai an nada sabon mai mukamin. Sanarwar ta kuma umarci Abdullahi Musa da ya mika ragamar ofishin ga wadda za ta rike mukamin kafin ko a ranar Laraba, 11 ga Maris, 2026.

