Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta samu sahihan bayanan sirri daga Kwamitin Tsaro na Jiha cewa wasu na yunkurin haddasa rikici da tayar da zaune tsaye a lokacin bukukuwan Eid-el-Fitr na bana. Saboda haka ta ce ba za ta yi wasa da alhakin da kundin tsarin mulki ya dora mata na tabbatar da doka, oda da kare rayuka da dukiyoyin al’umma ba.
Bayan tattaunawa da Majalisar Masarautar Kano da sauran masu ruwa da tsaki, gwamnati ta amince Hawan Idi zai gudana karkashin jagorancin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II daga filin idi na Kofar Mata zuwa Gidan Shettima, sannan a kammala a Kofar Fatalwa ta fadar sarki. Haka kuma, Hawan Nasarawa zai gudana ne a mota ba tare da hawa dawakai ba.
Sai dai gwamnati ta sanar da dakatar da Hawan Daushe, Hawan Fanisau da Hawan Dorayi na wannan karo domin maslahar zaman lafiya da tsaron jama’a. Ta kuma umurci dukkan hukumomin tsaro su tsaurara sa ido tare da daukar duk matakan doka domin hana duk wani yunkurin tayar da hankali kafin, lokacin da kuma bayan Sallah.

