Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Alhamis 19 da Juma’a 20 ga Maris, 2026 a matsayin hutun ƙasa domin bikin Eid al-Fitr. Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya sanar da hakan a madadin gwamnati ta bakin sakatariyar ma’aikatar, Dr Magdalene Ajani, a ranar Talata.
Ministan ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan, tare da kira gare su da su ci gaba da riƙo da kyawawan ɗabi’u kamar soyayya, kyautatawa, haƙuri da sadaukarwa da aka koyar a watan. Ya kuma buƙaci dukkan ‘yan Najeriya su yi amfani da lokacin wajen yi wa ƙasa addu’ar zaman lafiya da haɗin kai.
Haka kuma ya shawarci jama’a da su gudanar da bukukuwan cikin natsuwa tare da taimaka wa masu buƙata a cikin al’umma. Ya jaddada cewa Gwamnatin Tarayya na ci gaba da ƙoƙarin ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya a tsakanin ‘yan Najeriya baki ɗaya.
Add A Comment

