Wasu ‘yan Najeriya na daga cikin mutane da dama da suka jikkata bayan Iran ta sake harba makamai masu linzami da jirage marasa matuki kan wuraren da ke da alaƙa da Amurka a United Arab Emirates. Rahotanni sun ce harin ya yi sanadin mutuwar mutane shida tare da jikkata sama da 140.
Ma’aikatar tsaron UAE ta bayyana cewa rundunar kare sararin samaniyarta ta dakile wasu makamai masu linzami guda tara da kuma jirage marasa matuki 33 da aka harba ranar 14 ga Maris. Ta ce daga cikin wadanda suka mutu akwai ‘yan kasar UAE da kuma baki daga kasashe kamar Pakistan, Nepal da Bangladesh, yayin da wasu ‘yan kasashe da dama ciki har da Najeriya suka jikkata.
Harin ya kara tayar da hankali a yankin Gabas ta Tsakiya, inda ake zargin Iran ta kai hare-haren ne a matsayin ramuwar gayya kan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai mata. A halin yanzu wasu ‘yan Najeriya da ke yankin Gulf sun bukaci gwamnatin Najeriya ta shirya yiwuwar kwaso ‘yan kasar idan rikicin ya kara tsananta.
Add A Comment

