Hukumar Kiyaye Afkuwar Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ta ce mutane 110 sun rasa rayukansu a hatsarin mota 234 da aka samu a Jihar Neja tsakanin watan Janairu zuwa Yuli 2026.
Kwamandan FRSC ta jihar, Aishat Sa’adu, ce ta bayyana hakan a Minna yayin bikin ɗaga darajar jami’ai 18 da aka yi wa karin matsayi. Ta ce hatsarin ya shafi motoci 309 da mutane 1,938, yayin da mutane 892 suka samu raunuka.
Sa’adu ta ce daga cikin hatsarin, 62 sun yi sanadin mutuwa, 169 kuma masu tsanani ne, yayin da uku suka kasance ƙananan hatsarori. Ta ƙara da cewa a shekarar 2025 an samu hatsari 233 da suka yi sanadin mutuwar mutane 229 da jikkatar 1,109.
Kwamandan ta ce an samu raguwar mace-mace a bana sakamakon wayar da kan masu amfani da hanya da kuma sintiri na yau da kullum. Ta ce daga cikin abubuwan da ke haddasa hatsarin akwai wuce gona da iri wajen ƙetare motoci, ɗaukar kaya fiye da kima da kuma gudun wuce gona da iri.

