Hedkwatar Tsaron Najeriya ta ƙaddamar da wani sabon gaggarumin aikin soji mai suna Operation Clean Sweep III a ƙaramar hukumar Matazu da ke jihar Katsina domin yaƙar ƴan ta’adda da masu garkuwa da mutane.
An fara aikin ne bayan mutuwar tsohon Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, wanda ya rasu a hannun ƴanbindigar da suka yi garkuwa da shi tare da matarsa. Rundunar ta ce an fara aikin a ranar 14 ga Yuni, 2026 domin kamo masu hannu a lamarin da kuma lalata hanyoyin ayyukansu.
Sojojin sun bayyana cewa tun bayan ƙaddamar da aikin, suna gudanar da sintiri, kai hare-hare bisa bayanan sirri da kuma bincike a wuraren da ake zargin ƴan ta’adda na ɓoye. Haka kuma, sun jaddada cewa za su ci gaba da matsa lamba har sai an cimma manufar aikin, yayin da aka binne marigayi Janar Rabe Abubakar a makabartar Gidan Dawa da ke Katsina.

