Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya bayyana dalilin goyon bayansa ga tikitin Musulmi da Musulmi, yana mai cewa hakan ya samo asali ne daga buƙatar inganta shugabanci da ci gaban ƙasa.
Jingir ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a taron Northern Muslims Intellectuals Forum da aka gudanar a Jihar Jigawa, inda ya yi bayani kan ce-ce-ku-ce da kalaman da ya yi a wata ziyara da ya kai Kano suka haifar.
Ya ce goyon bayansa ga tikitin Musulmi da Musulmi ya haifar da adawa daga wasu mutane, amma ya jaddada cewa matsayinsa bai kasance domin zagi, ƙirƙirar ƙarya ko karya alƙawari ba. Ya ce yana goyon bayan gwamnatin Tinubu ne saboda tikitin Musulmi da Musulmi da kuma ci gaban da ya ce gwamnatin ta kawo.
Sheikh Jingir ya kuma ce a baya Musulmi sun fuskanci bincike da tsangwama a wasu wurare a Jos, yayin da a halin yanzu ya ce yanayin ya sauya. Ya bayyana cewa duk da ba za a ce komai ya yi daidai ba, a ganinsa gwamnatin Tinubu ta yi abin a yaba.

