Jami’an hukumar ICPC sun cigaba da tsare tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, jim kaɗan bayan kammala zaman kotu a Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna. An ce sun tafi da shi ne cikin mota zuwa Abuja bayan sauraron buƙatar belinsa.
Rahotanni sun nuna cewa an tsaurara matakan tsaro a harabar kotun tun kafin fara zaman, lamarin da ya haifar da hasashen cewa za a iya hana belin nasa. El-Rufai ya isa kotu da misalin ƙarfe 9:05 na safe, inda ya jawo hankalin jami’an tsaro da masu kallo.
Lauyan da yake kare El-Rufai, Oluwole Iyamu (SAN), ya tabbatar da cewa kotu ta ɗage yanke hukunci kan belin zuwa ranar 14 ga Afrilu. Ya kuma ce suna da wani shari’a daban da za a saurara a ranar 10 ga Afrilu a Abuja, yayin da tsaro ya hana ‘yan jarida shiga cikin kotun.

