Babbar Kotun Tarayya da ke Maitama ta bayar da umarnin tsare tsohon Shugaban Kotun Da’a ta CCT, Danladi Umar, a Gidan Gyaran Hali na Kuje bayan EFCC ta gurfanar da shi kan tuhume-tuhume hudu da suka shafi cin hanci da amfani da mukami ba bisa ka’ida ba.
Gwamnatin Tarayya ta zarge shi da karɓar Naira miliyan 5.5 da Naira miliyan 6 ta asusun bankin matarsa daga wasu ‘yan kwangila, tare da umartar wani ɗan kwangila ya biya Naira miliyan 2.43 kuɗin makarantar ‘yarsa a Jami’ar Baze da ke Abuja. Sai dai Umar ya musanta dukkan tuhume-tuhumen.
Mai shari’a Peter Kekemeke ya ɗage sauraron buƙatar belin zuwa ranar 15 ga Yuli, bayan masu gabatar da ƙara sun ce suna buƙatar lokaci domin mayar da martani kan takardar neman belin da lauyan wanda ake tuhuma ya gabatar.

