Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta soke rajistar jam’iyyun siyasa guda biyar, waɗanda suka haɗa da ADC, Accord, AA, APP da ZLP.
Mai Shari’a Peter Lifu ne ya yanke hukuncin bayan wata ƙungiyar tsofaffin ‘yan majalisu ta shigar da ƙara tana neman a tilasta wa INEC aiwatar da tanadin doka kan jam’iyyun da suka gaza cika wasu sharuɗɗan da kundin tsarin mulki ya tanada.
Masu ƙarar sun ce jam’iyyun sun kasa samun kaso 25 cikin 100 na ƙuri’u ko kujerun gwamnati kamar yadda doka ta tanada. Hukuncin na iya yin tasiri ga shirye-shiryen zaɓen shekarar 2027, musamman ga masu neman takara a ƙarƙashin waɗannan jam’iyyu.

