Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta kara mafi karancin albashin sojojin Najeriya zuwa Naira 100,000 a wata, bayan yin duba kan walwala da jin dadinsu. Sai dai ya ce har yanzu kasafin da ake ware wa bangaren tsaro bai wadatar ba.
Ministan ya kuma bukaci a tanadi hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane domin dakile yawaitar wannan laifi. Ya ce dokokin da ake da su a yanzu ba su da tsauri, lamarin da ke bai wa masu aikata laifuka damar ci gaba da ta’addanci.
Har ila yau, Musa ya ce masu garkuwa da daliban Oyo na kokarin tilasta wa sojoji sakin wasu kwamandojinsu da ake tsare da su. Ya kuma musanta zargin cewa ana ba sojoji abinci mara kyau, yana mai cewa an yi amfani da wata bidiyo wajen karkatar da gaskiya.

