Rahotanni sun nuna cewa matsalar rashin wutar lantarki na kara tsananta a fadin Najeriya, inda gidaje da ‘yan kasuwa ke fama da tsadar rayuwa sakamakon hauhawar farashin fetur da dizal tare da rashin ingantacciyar wuta. A birane kamar Kano, Kaduna, Legas da Kwara, jama’a sun koka kan yadda matsalar ke durkusar da harkokinsu.
Mazauna Kano sun bayyana cewa wutar lantarki ta kara tabarbarewa, inda wasu suka ce ba sa samun wuta kwata-kwata duk da biyan kudade masu tsada. ‘Yan kasuwa kanana sun ce suna shan wahala musamman a lokacin zafi, yayin da wasu suka koma amfani da kankara ko janareto domin ci gaba da kasuwanci, duk da tsadar mai.
Ministan lantarki, Adebayo Adelabu, ya nemi afuwar ‘yan Najeriya kan halin da ake ciki, yana mai alkawarin samun sauki cikin makonni biyu, amma da dama sun nuna shakku kan hakan. Masana tattalin arziki sun ce haduwar rashin wuta da tsadar mai na kara jefa tattalin arziki cikin matsala.

