Sama da mutum 3,000 mazauna Unguwar Guru da ke Ƙaramar Hukumar Kankia a Jihar Katsina sun bar gidajensu sakamakon yawaitar hare-haren ’yan bindiga. A yanzu haka suna samun mafaka a gine-ginen da ba a kammala ba, makarantu da gidajen ’yan uwansu.
Sabbin hare-haren sun faru ne ranar Asabar da Litinin, inda aka kashe mutane 13 tare da sace wasu mata da ’yan mata. Mazauna yankin sun ce sun shafe sama da kwanaki tara a garin Rimaye, bayan sun bar gidajensu ba tare da ɗaukar komai ba.
Mazauna sun ce har yanzu ba su samu tallafi daga gwamnatin jihar ko ta tarayya ba, inda suka roƙi gwamnati ta samar musu da abinci, ruwa, tufafi da sauran kayan agaji. Sun kuma ce an ƙone wasu gidaje, yayin da iyalai suka rabu kuma wasu ba su san inda ’yan uwansu suke ba.
Gwamnatin Jihar Katsina ta ce tana jiran cikakken rahoto daga hukumomin yankin kafin ta yanke shawarar matakin da ya dace. Gwamnatin ta ce ta fahimci halin da mutanen da suka rasa matsugunansu ke ciki, tare da gode wa al’ummomin da suka ba su mafaka.

