Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa cire tallafin mai da sauye-sauyen tsarin canjin kudaden waje (FX) sun samar da karin kudaden shiga da suka kai Naira tiriliyan 15.8 tsakanin Yuni 2023 da Disamba 2025.
Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Tattalin Arziƙin Ƙasa, Taiwo Oyedele, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai kan sakamakon sauye-sauyen gwamnatin Najeriya. Gwamnatin ta ce jihohi da ƙananan hukumomi ne suka samu kaso mafi yawa daga cikin wadannan kudade, sakamakon yadda aka samu karin kudaden da ake rabawa tsakanin matakan gwamnati na kasar.
Oyedele ya bayyana cewa ba a saka kuɗin a Asusun Tarayya a matsayin wani layi na musamman mai suna “subsidy savings” ba. A cewarsa, tasirin sauye-sauyen ya bayyana ne ta hanyar ƙarin kuɗin shiga da aka samu sakamakon sauyin farashin canjin kuɗi da kuma cire gurɓatattun hanyoyin da tallafin man ya haifar.
Ministan ya ƙara da cewa sauyin tsarin canjin kuɗi ma ya kawo ƙarin albarkatu, saboda a baya gwamnati tana ba da wani tallafin ɓoye ga tsarin canjin kuɗi. Ya ce wannan tallafin ba ya zuwa ga talakawa ko masana’antu, sai dai masu cin gajiyar bambancin farashin canji.

