Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa za ta nemi a biya diyya kan dukiya da wuraren kasuwancin ’yan ƙasarta da suka bari a Afirka ta Kudu, bayan da aka kwaso su gida sakamakon hare-haren nuna ƙyamar baƙi. Muƙaddashin Babban Jakadan Najeriya a ƙasar, Alexander Ajayi, ne ya bayyana hakan.
Ajayi ya ce gwamnati ta fara tattara bayanai kan kadarorin da ’yan Najeriya suka bari, domin tuntubar gwamnatin Afirka ta Kudu kan batun diyya. Ya ƙara da cewa an umarci waɗanda suka dawo su bayyana cikakken bayanin dukiyoyinsu da suka haɗa da kantuna, motoci da sauran kadarori.
A halin yanzu, wasu karin ’yan Najeriya 271 sun isa filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas bayan an kwaso su daga Afirka ta Kudu. BechiHausa ta ruwaito cewa sun gargaɗi sauran ’yan ƙasar da su guji tafiya can, bayan sabbin zanga-zangar ƙyamar baƙi da aka gudanar a ƙasar.

