Ministan Ƙaramar Harkokin Tsaro, Bello Matawalle, ya ce yana taya gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, murnar zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), bayan sauya sheƙarsa daga Peoples Democratic Party (PDP). Matawalle ya bayyana sauyin a matsayin muhimmin lamari a siyasar Zamfara da Najeriya baki ɗaya.
A cikin wani saƙon maraba da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Matawalle ya ce sauyin zai taimaka wajen haɗa ƙarfi domin tinkarar matsalolin tsaro da kuma bunƙasa ci gaban Jihar Zamfara.
Ya kuma ce shigar Lawal cikin APC zai ƙarfafa kokarin aiwatar da ajandar “Renewed Hope” ta shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, tare da kira ga ‘ya’yan jam’iyyar APC a Zamfara su haɗa kai domin samun nasara a zaɓen shekarar 2027.

