Shugaban jam’iyyar NDC na Najeriya, Sanata Seriake Dickson, ya bayyana cewa ƙofar jam’iyyarsu a buɗe take domin tattaunawa da sauran jam’iyyun hamayya gabanin zaɓen shekarar 2027.
Dickson ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels, inda ya ce jam’iyyar na maraba da duk wata tattaunawa da za ta inganta haɗin gwiwa tsakanin jam’iyyun adawa.
Sai dai ya jaddada cewa duk wata jam’iyya da ke neman haɗin gwiwa da NDC dole ne ta kasance a shirye wajen mara wa jam’iyyarsu baya a zaɓen 2027.

