Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ta kama hodar iblis, Canadian Loud da magungunan opioid da darajarsu ta haura naira biliyan 10 a farashin kasuwa, yayin wasu samame da ta gudanar bisa bayanan sirri a Legas da sauran sassan ƙasar.
Hukumar ta ce ta kama wani ɗan kasuwa mai shekaru 55, Onuigbo Ndubisi Chinedu, bisa zargin ƙoƙarin fitar da kilo 3.30 na hodar iblis da aka ɓoye cikin kwali na kayan abinci zuwa Birtaniya. Ta kuma ce bincike ya kai ga gano shi a matsayin jagoran wata ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi.
A wani samamen daban, NDLEA ta cafke Emmanuella Chukwu-Edo mai shekaru 31 bayan kama wani kunshin kilo 2.80 na Canadian Loud da aka shigo da shi daga Amurka. Haka kuma ta ƙwace ƙwayoyin Tapentadol 250mg guda miliyan 2.24 da darajarsu ta haura naira biliyan 2.2, waɗanda aka shigo da su daga Indiya.
A tashar jiragen ruwa ta Apapa kuwa, jami’an NDLEA sun gano buhuna 4,777 na Canadian Loud masu nauyin kilo 2,388.5 da darajarsu ta haura naira biliyan 7.1, waɗanda aka ɓoye cikin motoci uku da aka shigo da su. A Jihar Katsina kuma, hukumar ta kama Mustapha Sani da harsasai 323 na manyan bindigogi a Ƙaramar Hukumar Safana.

