Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    BECHI HAUSA NEWSBECHI HAUSA NEWS
    • Shafin Farko
    • Labarai

      Najeriya Ta Musanta Zargin Goyon Bayan Yunƙurin Juyin Mulki a Nijar

      September 4, 2026

      A shirye nake na mutu domin kare ƙuri’ata – Peter Obi

      September 4, 2026

      Sarkin Gumel Alhaji Ahmed Muhammad Sani Ya Rasu 

      September 3, 2026

      Gwamnatin Kano ta fitar da iyakoki tsakanin Jam’iar Bayero da alummar Rimin Zakara bayan kammala biyan diyya

      September 3, 2026

      Ƙungiyar Miyetti Allah Ta Buƙaci Tinubu Ya Sa a Saki Shugabanta

      September 3, 2026
    • Siyasa

      A shirye nake na mutu domin kare ƙuri’ata – Peter Obi

      September 4, 2026

      Ɗan Takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a NDC Na Shirin Komawa APC

      September 2, 2026

      Ƴan Siyasa Ne Matsalar Najeriya – Peter Obi

      August 31, 2026

      Bai kamata Tinubu ya bar Najeriya a dai dai lokacin da matsaloli ke addabar ƙasarsa ba – Atiku

      August 31, 2026

      Atiku Ya Yi Alkawarin Sake Buɗe Iyakokin Najeriya Idan Ya Lashe Zaɓen 2027

      August 28, 2026
    • Addini

      Shugaban Asibitin Kwararru na Best Choice, Na Taya Gwamnan Kano Da Al’umma Bikin Murnar Maulidi Annabi SAW

      September 2, 2026

      Hajj 2027 : Kano ta kammala sayar da kujeru 3,050 da aka ware wa jihar

      August 31, 2026

      Gwamnatin Kano ta bayar da hutu domin bikin Takutaha

      August 26, 2026

      Wasu Malamai Daga Arewacin Najeriya Sun Goyi Bayan Tazarcen Tinubu

      August 23, 2026

      Gwamnatin Tarayya ta ayyana Talata a matsayin ranar hutun Maulidi

      August 21, 2026
    • Nishadi

      Oculus Founder Makes a VR Headset That Can Literally Kill You

      January 13, 2021
      85

      Braun Series 7 Electric Shaver Review: Quality at a Good Price

      January 13, 2021
      85

      Google Pixel 7, iPhone 14 Compared: Check Out 5 Major Differences

      January 13, 2021

      Why Apple Should Skip The MacBook Pro Launch

      January 12, 2021

      Apollo G2J Showcases Electric Sports Car

      January 12, 2021
    • Tsaro

      Ƴanbindiga Sun Sace Shugaban Jam’iyyar ’iyyar APC Na Ƙaramar Hukumar Rogo

      September 1, 2026

      Amurka Za Ta Janye Sojoji Kusan 200 Daga Najeriya

      August 28, 2026

      Sojoji Sun Kama Ƴan Ƙasashen Waje Da Ake Zargin Suna da Hannu a Matsalar Tsaron Najeriya – Bwala

      July 18, 2026

      ‘Yan Sanda Sun Fara Kwato Makaman Da Ke Hannun Jama’a Ba Bisa Ka’ida Ba – IGP Disu 

      July 17, 2026

      Sojoji Sun Gano Ƴan Ƙasashen Waje Uku Cikin Mayaƙan ISWAP a Borno

      July 13, 2026
    BECHI HAUSA NEWSBECHI HAUSA NEWS
    Home » NEMA Ta Karɓi Ƴan Najeriya 153 Da Suka Makale a Chadi
    Featured

    NEMA Ta Karɓi Ƴan Najeriya 153 Da Suka Makale a Chadi

    Abbass AbdurrahmanBy Abbass AbdurrahmanOctober 28, 2025Updated:October 28, 2025No Comments2 Mins Read

    Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta karɓi ‘yan Najeriya 153 da suka makale a ƙasar Chadi karkashin shirin dawowa gida (Assisted Voluntary Return Programme) wanda Ƙungiyar Kula da Ƙaura ta Duniya (IOM) ke gudanarwa tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Tarayya. Jirgin ASKY Airlines mai lamba CAS-AC ne ya sauke su a filin jirgin saman Murtala Muhammed, Legas, da misalin ƙarfe 12:15 na rana, ranar Lahadi, 27 ga Oktoba, 2025.

    Bayanan da hukumar ta fitar sun nuna cewa cikin waɗanda suka dawo akwai manya 105 (maza 63 da mata 42), yara 45 (maza 25 da mata 20), da kuma jarirai uku mata. Bayan isowarsu, jami’an Hukumar Shige da Fice (NIS) sun gudanar da rajista da tantance su domin samun sahihin bayanai da sauƙaƙa musu komawa rayuwa cikin sauƙi.

    NEMA ta bayyana cewa an ba wa waɗanda suka dawo taimakon gaggawa kamar abinci, ruwa, kula da lafiya, da motar daukar marasa lafiya, tare da shawarwari da goyon baya. Hukumar ta ce wannan mataki na cikin ƙoƙarin gwamnatin tarayya na tabbatar da dawowar ‘yan ƙasa cikin mutunci da aminci, ba tare da wahala ba.

    Rahoton ya ƙara da cewa wannan ba shi ne karon farko ba, domin kwanaki kaɗan da suka gabata ma, NEMA ta karɓi wasu ‘yan Najeriya 150 daga Agadez, Jamhuriyar Nijar, karkashin irin wannan shiri. Hukumar ta tabbatar da cewa tana ci gaba da haɗin gwiwa da IOM da Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira da Masu Hijira (NCFRMI) domin taimaka wa dubban ‘yan Najeriya da suka makale a ƙasashen waje su koma gida cikin mutunci.

    Chadi
    Share. Facebook Twitter WhatsApp Telegram
    Previous ArticleTInubu Ya Buƙaci Majalisar Dattawa Ta Amince Da Naɗin Sabbin Hafsoshin Tsaro
    Next Article Yan Sanda Sun Kama Masu Fashi da Makami a Bauchi
    Abbass Abdurrahman
    • Website

    Related Posts

    Featured

    Najeriya Ta Musanta Zargin Goyon Bayan Yunƙurin Juyin Mulki a Nijar

    September 4, 2026
    Featured

    A shirye nake na mutu domin kare ƙuri’ata – Peter Obi

    September 4, 2026
    Featured

    Sarkin Gumel Alhaji Ahmed Muhammad Sani Ya Rasu 

    September 3, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    SABBIN LABARAI

    Ba Don Gudunmawar Masu Yiwa Ƙasa Hidima Ba Da Jihohi Dayawa Basu Kai Yadda Suke a Yanzu Ba – Minista

    December 8, 2025229 Views

    Sabon Rikici Ya Kunno Kai a NDC : Ƴan Takara Sun Kai Ƙara Kan Zaɓen Fidda-gwani a Kano

    June 30, 202680 Views

    Gwamnatin Kano Ta Dakatar da Malam Lawan Triumph Daga Yin Wa’azi

    October 1, 202551 Views

    Gwamnatin Kano Ta Raba Filaye Ga Masu Taimakawa Gwamna Sama da 2,500

    August 1, 202644 Views

    Kotu Ta Yankewa Tsohon Firayim Ministan Mali Hukuncin Zaman Gidan Yari Sakamakon Rubutu a Shafin Sada Zumunta

    October 27, 202541 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    • Telegram
    © 2026 Bechi Hausa News. Developed by: ENGRMKS & CO.
    • Shafin Farko
    • Game da Mu
    • Ƙarin Bayani
    • Manufar Sirri
    • Ka’idoji da Sharudda
    • Tuntuɓe Mu

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.