Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kare rabon filaye da gwamnatinsa ke yi ga wasu rukunin al’umma, yana mai cewa manufar shirin ita ce rage ƙarancin gidaje, ƙarfafa mallakar kadarori da inganta tattalin arzikin iyalai.
Gwamnan ya bayyana hakan ta bakin Sakataren Gwamnati, Alhaji Umar Ibrahim, yayin bikin rabon takardun mallakar filaye ga manyan mataimaka na musamman, mataimaka na musamman da masu rahoto na musamman na gwamnatin jihar.
Abba ya ce mallakar fili na taimaka wa mutane wajen gina gidaje, tara dukiya da samar wa iyalansu kyakkyawar makoma. Ya ƙara da cewa shirin zai ba matasa, mata da sauran marasa galihu damar mallakar kadarorin da za su amfane su a nan gaba.
Sai dai rabon filayen ya jawo ce-ce-ku-ce a Kano, musamman bayan sanarwar rabon filaye 1,540 da tallafin Naira miliyan 100 ga shugabannin masu zaɓe na APC da aka fi sani da ‘Yan Akwati. Wasu mazauna jihar sun ce matakin na iya kasancewa neman goyon bayan masu zaɓe gabanin 2027, zargin da gwamnatin jihar ta musanta.

