Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta ce sabon rahoton da ya nuna cewa talauci a Najeriya ya kai kashi 63 cikin ɗari bayan cire tallafin man fetur shi ne ainihin sakamakon manufofin tattalin arzikin Shugaba Bola Tinubu. Jam’iyyar ta ce karin farashin mai da sufuri ya ƙara tsananta rayuwa ga miliyoyin ‘yan ƙasar.
A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya sanya wa hannu, ADC ta ce rahoton ya nuna yadda talauci ya tashi daga kusan kashi 50 kafin cire tallafin mai zuwa kashi 63 bayan an cire shi. Ta ce tsadar man fetur da sufuri ne ya haifar da tashin farashin abinci da sauran muhimman kayayyakin rayuwa.
Jam’iyyar ta kuma ce duk da cewa gwamnati ta yi hujjar cewa cire tallafin mai zai ba da damar zuba kuɗi a fannoni kamar lafiya da ilimi, amma shekaru uku bayan haka babu wani gagarumin ci gaba da jama’a suka gani. ADC ta ce a ma’aunin ko manufofin tattalin arziki sun inganta rayuwar jama’a ko a’a, gwamnatin APC ta gaza.

