Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi Allah-wadai da kashe-kashen da suka faru a jihohin Plateau da Kaduna, yana mai cewa gwamnatinsa na sayen sabbin kayan aiki na zamani domin bai wa jami’an tsaro damar gano da kuma murƙushe masu aikata laifi a kowane lokaci.
A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya tabbatar da cewa hukumomin tsaro za su hukunta duk waɗanda ke da hannu a hare-haren. ‘Yan bindiga sun kai farmaki a Jos da kuma wata ƙauye a Kaduna inda suka kashe mutane tare da sace wasu.
Shugaban ya jajanta wa iyalan waɗanda abin ya shafa tare da umartar jami’an tsaro su ƙara ƙaimi wajen cafke masu laifi da kuma dakile yaɗa jita-jita. Ya kuma buƙaci al’umma su ba da haɗin kai, yana mai yabawa gwamnonin Plateau da Kaduna kan matakan da suka ɗauka wajen shawo kan lamarin.

