Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ayyana yau Juma’a, 14 ga Agusta, 2026, a matsayin ranar 1 ga watan Rabi’ul Auwal na shekarar 1448AH a Najeriya.
Wazirin Sokoto, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, 13 ga Agusta, 2026.
Sanarwar ta ce Kwamitin Ba da Shawara kan Harkokin Addini na Majalisar tare da Kwamitin Duban Wata sun samu rahotannin ganin sabon watan a sassa daban-daban na Najeriya.
Rahotannin sun nuna cewa an ga watan ne ranar Alhamis, 13 ga Agusta, 2026, wadda ta kasance 29 ga Safar 1448AH. Sarkin Musulmi ya amince da rahotannin tare da ayyana Juma’a, 14 ga Agusta, a matsayin 1 ga Rabi’ul Auwal 1448AH.

