’Yan bindiga sun kashe wasu mutane biyu tare da jagorantar Sallar Juma’a a Babban Masallacin Izalah da ke ƙauyen Kaya, a Ƙaramar Hukumar Tambuwal ta Jihar Sakkwato.
Jaridar Aminiya ta rawaito cewa, wani mazaunin ƙauyen ya ce maharan sun shiga garin da misalin ƙarfe 11 na safe, inda suka kwashe kusan sa’o’i bakwai suna kai hare-hare ba tare da fuskantar turjiya ba. Sun tilasta wa mazauna zama a gidajensu, yayin da suke shiga gida-gida suna satar shanu.
A lokacin Sallar Juma’a, ’yan bindigar sun nufi masallacin, suka yi kiran sallah tare da jagorantar sallar. Bayan kammala sallar kuma, sun shiga shaguna da kai wa masu POS hari, inda suka kwashe kuɗaɗe har na miliyoyin Naira, ciki har da sama da Naira miliyan shida daga hannun wani mai POS.
Shaidan ya ce maharan sun kashe Maijega Sarkin Baka da Umar, sannan suka kwashe sama da shanu 500. Ya ce sun sake dawowa washegari suka ƙara kwashe wasu shanu, lamarin da ya sa mazauna yankin ke neman hukumomi su ƙara tsaurara matakan tsaro.

