Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta sanar da kammala jigilar alhazan Najeriya sama da 38,000 da suka gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026 a ƙasar Saudiyya. Hukumar ta ce ana sa ran jirgin ƙarshe ɗauke da alhazan Jihar Zamfara zai iso ƙasar nan a ranar Talata.
A cikin sanarwar da mai magana da yawun hukumar, Hajiya Fatimah Usara, ta fitar, ta bayyana cewa kammala jigilar alhazan ya kawo ƙarshen ayyukan Hajjin 2026 a hukumance.
Sai dai ta ce alhazai 12 na Najeriya har yanzu suna karɓar magani a asibitoci daban-daban na Saudiyya. Ta ƙara da cewa hukumar na sa ido kan lafiyarsu tare da shirya yadda za a dawo da su gida cikin koshin lafiya, yayin da ta ce an fara shirye-shiryen Hajjin 2027 domin ƙara inganta ayyukan hajji a gaba.

