Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya amince da sanya dokar hana fita ta sa’o’i 16 a wasu ƙananan hukumomi 10 na jihar sakamakon matsalolin tsaro da ake fuskanta a yankunan.
A cikin sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Musibau Babatunde, ya fitar, an bayyana cewa dokar za ta fara aiki daga yau Laraba, 24 ga Yuni, 2026, daga ƙarfe 4:00 na yamma zuwa ƙarfe 8:00 na safe a matakin farko.
Ƙananan hukumomin da dokar ta shafa sun haɗa da Oriire, Orelope, Irepo, Saki West, Saki East, Atisbo, Itesiwaju, Iseyin, Olorunsogo da Atiba, musamman yankunan da ke kusa da gandun dajin Old Oyo National Park, bayan zanga-zangar da ta biyo bayan sace yara da malamai a yankin Oriire a watan Mayu.

