Gwamnatin Jihar Oyo ta sanar da janye dokar hana fita da ta sanya a ƙananan hukumomi 10, biyo bayan sace mutane da aka yi a yankin Oriire. Tun farko an kafa dokar ta sa’o’i 16, kafin daga bisani aka tsawaita ta da wani yini domin magance matsalolin tsaro.
A cikin wata sanarwa, Kwamishinan Watsa Labarai, Prince Dotun Oyelade, ya ce mazauna yankunan da abin ya shafa za su iya komawa gudanar da harkokinsu na yau da kullum. Ya kuma yabawa al’umma bisa haɗin kai da fahimtar juna da suka nuna a lokacin da dokar ke aiki.
Oyelade ya tabbatar da cewa gwamnati na ci gaba da sanya ido kan harkokin tsaro domin shawo kan matsalar sace mutane. Lamarin ya samo asali ne daga harin da ‘yanbindiga suka kai makarantu uku a Oriire ranar 15 ga Mayu, inda suka sace ɗalibai da malamai 45, yayin da daga baya aka tabbatar da mutuwar ɗaya daga cikin malaman da aka sace.

