Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, ya buƙaci iyaye su hana ‘ya’yansu almubazzaranci wajen bukukuwan aure, musamman kashe kuɗaɗe masu yawa kan kwalliya da kayan aso-ebi. Ya ce ya fi dacewa a karkatar da irin waɗannan kuɗaɗe wajen tallafa wa mabukata da ƙungiyoyin agaji.
Sarkin ya bayyana hakan ne a bikin cika shekara 20 da kafuwar Crystal Muslim Organisation (CMO) a Abuja. Ya ce yawaitar kashe kuɗi kan abubuwan jin daɗi a lokacin da mutane da dama ke fama da talauci na ƙara haifar da matsalolin zamantakewa, yana mai jaddada cewa shi bai taɓa kashe ko sisi kan aso-ebi ko kwalliyar aure ba.
Haka kuma, ya yi kira da a haɗa koyar da sana’o’i cikin manhajar makarantun Boko da Islamiyya domin ɗalibai su dogara da kansu bayan kammala karatu. Kungiyar CMO ta ce bikin ya kasance domin murnar cika shekara 20 da kafuwarta tare da karrama ɗalibai 12 da suka yi fice a gasar rubutu.

