Shuaib Abubakar Fagge, Mustapha Salisu Musa (Fanandas), Musa Hudu Yusuf, Mukhtar Muhammad (mai neman takarar gwamna) da Mahfuz Yahuza sun kai ƙara a Babbar Kotun Tarayya suna ƙalubalantar halaccin zaben fidda gwani da jam’iyyar NDC ta gudanar a Jihar Kano ranar 28 ga Mayu, 2026. Sun roƙi kotu ta soke zaben tare da hana Hukumar INEC amincewa da sunayen ‘yan takarar da suka fito daga cikinsa.
Masu ƙarar sun yi zargin cewa jam’iyyar ta karya dokar zaɓe, kundin tsarinta da ƙa’idojinta, inda suka ce an ba mutum ɗaya ikon sayarwa da rarraba fom ɗin takara, sannan aka hana su samun fom duk da sun cika sharuɗɗa. Sun kuma ce ba a gudanar da sahihin zaben fidda gwani ba, domin babu ingantacciyar tantance masu zaɓe, kaɗa ƙuri’a, ƙirga ko tattara sakamako kamar yadda doka ta tanada.
Masu ƙarar suna neman a soke dukkan zaben fidda gwani na gwamna, na Majalisar Wakilai da na Majalisar Dokokin Jihar Kano, tare da soke takardar shaidar takarar da aka bai wa Aminu Suleiman Goro na mazabar Fagge. Haka kuma suna neman a tilasta wa NDC gudanar da sabon zabe bisa doka, yayin da ɗaya daga cikinsu ke neman a mayar masa da kuɗin fom na Naira miliyan 2 da kuma Naira miliyan 200 a matsayin diyya.

