Amurka ta sanar da janye yawancin dakarunta da ta tura Najeriya domin taimakawa yaƙi da ƙungiyar ISIS da sauran ƙungiyoyin ta’addanci a yankin Tafkin Chadi. Janar Dagvin R.M. Anderson ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, 3 ga Yulin 2026, bayan Taron Manyan Hafsoshin Tsaro na Afirka.
Janar Anderson ya ce an kammala aikin da aka tura dakarun domin yi, wanda ya sa aka mayar da yawancinsu Amurka. Sai dai ya tabbatar da cewa ƙasarsa za ta ci gaba da tallafa wa Najeriya ta hanyar musayar bayanan sirri da sauran taimakon da gwamnati za ta buƙata.
Ya ce haɗin gwiwar ƙasashen biyu ya taimaka wajen dakile ayyukan ISIS, ciki har da samamen da ya yi sanadin kashe wani mataimakin jagoran ƙungiyar a Borno. Janar Anderson ya buƙaci ƙasashen Afirka su ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa wajen yaƙi da ta’addanci da sauran laifukan da ke ƙetare iyakoki.

