Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ta bukaci a gaggauta cire Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, domin bai wa bincike mai zaman kansa damar gudana kan zarge-zargen da ke da alaƙa da hukumar Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC). Jam’iyyar ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a, 3 ga Yulin 2026.
NDC ta ce zarge-zargen sun haɗa da ikirarin ware kuɗi a kasafin 2026, buɗe asusu a Babban Bankin Najeriya (CBN), amincewa da ɗaukar ma’aikata da kuma zargin karɓar kuɗaɗe wajen naɗi. Jam’iyyar ta kuma buƙaci a binciki mutuwar Babatunde Tanimola da kuma zargin yunƙurin kashe Prince Mathew Adeniyi Adeyemi.
Sai dai Fadar Shugaban Ƙasa ta musanta zarge-zargen, tana mai cewa hukumar PFIPC babu ita, tare da zargin Adeyemi da ƙirƙirar takardun naɗi na bogi.

