Wani sabon rahoto na tsawon shekara shida da ƙungiyar Observatory for Religious Freedom in Africa (ORFA) ta fitar ya nuna cewa daga shekarar 2020 zuwa 2025, an kashe mutum 79,323 sakamakon hare-haren ta’addanci a Najeriya, yayin da aka yi garkuwa da fararen hula 34,773. An ƙaddamar da rahoton ne a ranar Talata a Jos.
Rahoton ya ce fararen hula 42,033 ne suka rasa rayukansu a lokacin, yayin da ya yi ikirarin cewa ƙungiyoyin da ya kira “Fulani Terror Groups” ne ke da alhakin kaso 44 cikin ɗari na kashe-kashen fararen hula, yayin da Boko Haram da ISWAP suka haddasa kaso 12 cikin ɗari. Sai dai ORFA ta jaddada cewa tana bambance tsakanin waɗannan ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da al’ummar Fulani gaba ɗaya.
Rahoton ya kuma bayyana cewa an kashe Kiristoci 28,551 da Musulmi 13,224, tare da yin garkuwa da Kiristoci 15,932 da Musulmi 15,272 a lokacin binciken. BechiHausa ta ruwaito cewa ORFA ta buƙaci a yi la’akari da dukkan abubuwan da ke haddasa rikicin domin samar da mafita mai ɗorewa ga matsalar tsaro a Najeriya.

